SHEKARA MAI BAN TSORO (2020),
ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜
Wannan Shekarar ta (2020) Abubuwan Jarabta Daga Allah masu yawa sun faru a Cikin ta, duk Wanda Allah Yayi wa tsawon Rai Bazai taba mantawa da ita ba bisa irin Abubuwan da suka Faru,
kuma Mai Hankali da tunani shi zai Dauki Darasi ya gane Cewa Duniyar nan Ba komai bace Face Qararriya, ya tsaya ya bautawa Allah kafin ya koma.
A wannan Shekarar ne Allah Ya Jarabci Duniya da wani Bala'i (Corona Virus) Wanda ya gajiyar da kwararrun Masu Fasahar kere kere Na Duniya,
A wannan shekarar Abubuwan Masu matukar mahimmanci ds suka Shafi Rayuwar mu sun tsaya Cak Misali, Bautar Ubangijin mu,kasuwanci,Ayyuka,Harkokin Ilimi, da sauran su,
A Wannan Shekarar Idan Baka rasa Wani naka ba to a unguwar ku An Rasa,Wasu sun rasa iyaye,kakanni 'Yan Uwa, mataye,'Ya'ya ye,Baffa ni da sauran su,
wato dai an samu Yawan mace mace,Masu Mulki sun mutu,Masu Sarauta sun mutu,Shahararun mutane sun mutu,Talakawa sun mutu,
kuma Har yau abin Kara Gaba yake don ko yau Naga sanarwar mutuwa da yawa,
Sannan mutane na Cikin Kangin Rashin Lafiya ga yunwa da Talauci, kuma gashi yanayin yaci karo da Lokacin Ibadar mu Mai Girma wato watan Ramadan,
Wadan da suka ninka mu a Shekaru ma Suna cewa Basu taba riskar irin wannan Lokacin ba Mai tarin hadari,
Mafita garemu shine abin da Malamai ke ta fada mana mutashi tsaye da neman gafarar Allah ,Yawaita Istigfari Salatin Annabi ( s,a,w) Zikiri karatun Al Qur'ani da Taimakon Mabukata sannan, mu daina aikata Saɓo muyi duk wani abu da zai kusanta mu Ga Allah.
