TAMBAYA TA 90

*Assalamu Alaikum*
.
.
*Tambayata 6,737:*
Shin menene gaskiyar labarinda ake yadawa cewa wai Sayyidina Aliyu yayi magana akan corona virus???
=
=
Amsa
=
_Majalisar koli ta fatawar kasar Misra na karanta bayanansu akan wannan magana wadda ake yadata a social media inda sukace wannan littafinda akace maganar tana cikinshi toh littafin a social media kawai ake ganinshi amma duk wani laburare na duniya wanda ake i'itibari dashi toh babu littafin kuma kaf malaman tarihi babu wanda yataba yin magana akan littafin wai sunan littafin *KITABU AZA'IMUD DUHUR* toh wannan littafin malaman tarihi basu sanshiba, hakama wanda akace ya wallafa littafin wai sunanshu Abi Ali Addubaizi. Toh malaman sukace shima wannan mutumin acikin littafan tarihi kaf babu inda zakaga anyi magana akanshi kaf malamanda akayisu a duniyar musulinci toh inka duba littafan tarihi zakaga anyi magana akansu amma shi wannan wanda akace ya wallafa littafinda acikin littafinne Sayyidina Aliyu yayi batun Corona toh babu wani daga cikin malaman tarihi wanda yayi magana akan wannan malamin, wato da malamin da littafin nashi dukkansu majahulaine. Toh abun tambaya shine daga ina aka samo littafin?? Sannan kuma su malaman sukace wata karin matsalar kuma shine larabcin wanda shine akace wai maganar sayyidina Aliyu toh larabcin cike yakeda Rakaka wanda shikuma Sayyidina Aliyu Baquraishe ne cikakken balarabe toh tayaya za,a kawo wannan larabcin irinna 'yan koyo kuma ace maganarsace. Duk mutuminda yasan larabci toh kana tura masa kace wannan maganar sayyidina Aliyu ce toh ze karyataka domin yana karanta larabcin yaga tarin kurakurai da suke cikinsa toh zece maka shi be yardaba. Kaga kenan mutuminda ya zauna ya tsara tatsuniyar da alamarma shidin kanshi jahiline bema gama sanin abunda yakeyiba amma yazo kawai ya tsara larabcinsa yana cewa wai sayyidina Aliyune ya fada. Mukuma dayake babu ruwanmu da tantance abubuwa da bin duddugi kawai semu kama turawa mutane bayan kuma Annabi (s.a.w) yace: Zunubi ya ishi mutum idan yazama duk abunda yaji seya bada labari****_
=
=
Allah Yasa mudace
 .
.
*DAGA ZAUREN*
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس تعليم الكتاب والسنة* 
📓📔 
Watsaps
08036222795
09031200070
.
°
Yau
05-ramadan-1441
28-04-2020
=
=
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
Domin samun shafinmu a Telegram 
https://t.me/joinchat/IqYRYUcyJstfI3sSYKPKsQ
°
Kuna iya samun tsoffin darussanmu kai tsaye ta cikin wannan shafin
http://www.zaurenkitabuwassunna.blogspot.com
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ. 
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka wa atubu ilaika

Post a Comment (0)