*🍝 GIRKE-GIRKEN ZAMANI 🍝*
*YADDA AKE ‘PAN CAKE’ DIN AYABA*
Akwai hanyoyi da dama na sarrafa ‘pan cake.’ Kowace mace na da irin nata yanayin sarrafa girki, shi ya sa a kullum nake kara tunatar da mu a kan cewa yana da kyau mace ta kasance mai sarrafa sabon abu a kullum. Koda tuwo ne, yana da kyau a kasance ana canja na’ukan miya domin kara wa abinci armashi da kuma kin fita ran masu ci. A yau na kawo muku yadda ake sarrafa ‘pan cake’ din ayaba. A ci dadi lafiya.
*Abubuwan da za a bukata*
· Ayaba
· kwai biyu
· Madara
· Bata
· Sukari
· Fulawa
*Yadda ake hadawa*
A samu na’urar markada kayan miya (blender), sannan a yayyanka ayabar a ciki. Bayan haka, sai a fasa kwai biyu a ciki, sannan a zuba bata (butter) kamar cokali uku zuwa hudu. Daga nan sai a zuba madarar ruwa ko a kwaba da madarar gari da ruwa sannan a zuba. A zuba sukari da garin fulawa kadan, sai a rufe na’urar a markada su, har sai sun yi laushi sannan a sha.
A dora tukunya mara kama girki a wuta (nonstick) bayan ta yi zafi, sai a rika debo kullun ayaba ana zuba shi ta irin yanayin da ake so. Idan ya dan nuna, sai a juya dayan gefen domin shi ma ya gasu. Sannan a kwashe. Za a iya cin wannan hadin da zuma ko da miya. Wannan abincin an fi yin sa ne a matsayin abincin karyawa.
*✍Written by admins*
*Sumayya &*
*Fauziyya*
*🍝 Girke-Girken Zamani 🍝*
*WhatsApp Group*
*0814 899 2840*
*0818 900 7071*
