TAMBAYA TA 84


📒📗 *TAMBAYA 44* 📗📒

https://darulfikr.com/ra/1042
Don Allah inda macce zatabi mijinta Sallah agida yaya zatayi kabbara Kuma don Allah inason aturomin Attahiyatu complete

*AMSA*
Wa alaikumussalaam wa Rahmatullahi wa Barakaatuh. Idan Mace za tayi jam'i da mijin ta ana so ta tsaya a bayan shi be, wannan shine sunnah kuma koyarwan Annabi(SAW), kamar yadda hadisai suka yi nuni akan hakan. Daga cikin su akwai hadisin Anas Bin Malik Allah Ya kara mishi yadda, wanda ya zo cikin Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim da Sunan da Muwadda'u, da sauran su, Anas Allah Ya kara mishi yadda yake cewa kakan shi Mulaikatu ta kira Manzon Allah(SAW) saboda abincin da tayi mishi ya zo gunta ya ci. Bayan ya zo ya ci sannan ya ce ku tashi in yi muku sallah sai Anas ya ce sai na tsaya a kan wata tabarma(shinfida) wadda tayi baki saboda lokaci mai tsawo da aka dauka ana anfani da ita sai na yayyafamata ruwa sai Manzon Allah(SAW) ya shiga gaba ya bamu sallah sai na tsaya ni da wani yaro a bayan Manzon Allah(SAW) sai wata mace tsohuwa (Ummu Sulaim) ta tsaya a bayan mu. Mallamai ma'abota ilimi sun fitar da fa'idoji masu yawa karkashin wannan hadisin, kadan daga ciki:
*(1)* Yayin da mutum zai yi sallah da matar shi ko wata mace, zata tsaya ne a bayan shi.
*(2)* Halascin yin sallar nafila cikin jam'i .

Amma Attahiyyaatu ta zo da sigogo dayawa a kalla za su kai shida (6), amma daga cikin sigar da ta fi shahara ita ce wanda ta zo cikin Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim wanda Abdullahi Ibnu Mas'ud Allah Ya kara mishi yadda,ya riwaito ta daga Annabi(SAW), 
 ( التحيات لله، والصلوات والطيبات، السلام على النبي ورحمة الله وبركاته،السلام علينا وعلى عبادالله الصالحين، أشهد أن لا إله إلا الله، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، )
Ana so mutum ya kara da salati ga Annabi(SAW) bayan ya gama Attahiyyaatu, Ita ma ta zo da sigogi da yawa zasu kai bakwai(7), daga cikin wanda ta shahara wanda ta zo cikin Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim da Sunanunnasaa'i da sauran su,
 ( اللهم صل على محمد، وعلى آل محمد، كما صليت على إبراهيم وعلى آل إبراهيم، إنك حميد مجيد، اللهم بارك على محمد وعلى آل محمد كما باركت على إبراهيم وعلى آل إبراهيم إنك حميد مجيد), Sannan Idan zaman karshe ne ana so ya
kara da wannan addu'ar kamar yadda Annabi(SAW), ya kasance yana yin ta
 (اللهم إني أعوذبك من عذاب جهنم، ومن عذاب القبر، ومن فتنة المحيا والممات، ومن شر فتنة المسيح الدجال، ومن المأثم والمغرم).

والله أعلم.
*DR NASIR YAHYA ABUBAKAR BIRNIN GWARI*
*13TH JULY 2020*
Post a Comment (0)