YADDA ZA KI RAGE TUMBI DA ƘIBA


*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Yadda Zaki Rage Ma Kanki Tumbi Ko Kiba_*

Ga masu dama da kiba ko tumbi wannan hadin na musamman ne wanda idan har kika hada shi to koda kina da kibarki zata rage, kayan hadin kamar haka;
* Garin hulba
* Ganyen na'a-na'a
* Garin kanunfari
* Zuma
* Lemun tsami
* Farin kwalli
* Man na'a-na'a
*Bayani;* zaki hade wadannan ganyen guri daya ki tafasa amma ban da lemun tsami, ki samu farin kwalli dunkulen daya ki saka a ciki, idan ya kai kamar minti biyar (5) sai ki cire, sannan ki saka zuma a cikin ruwan shan,kina sha lokaci lokaci, sai ki samu man na'a-na'a ki rinka shafawa a *TUMBI* don kawar da duhun tumbin in ya rage, insha Allah
Inda kuma ana son rage kiba ne za'a rinka zuba lemun tsami a ciki kina sha.


Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586 a WhatsApp.*
Post a Comment (0)