HUKUNCIN NAMIJIN DA BAYASAN HAIHUWA SABODA TSORAN DAWAINIYAR 'YA'YA



Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D3VpiJzm6WECmizK6DEBfi


✍🏻Daga Zauren 
      📌 *Albahral Ilmu*🌴

HUKUNCIN NAMIJIN DA BAYASAN HAIHUWA SABODA TSORAN DAWAINIYAR 'YA'YA



*TAMBAYA*❓

MENENE HUKUNCIN NAMIJIN DA BAYASAN HAIHUWA SABODA TSORAN DAWAINIYAR 'YA'YA, MENENE HUKUNCIN ZAMA DASHI, SHIN MATARSA ZATA IYA BIJIREMAR TADAU CIKI BATAREDA YASANI BA?
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﺃﻧﻌﻤﻨﺎ ﺑﻺﺳﻼﻡ .

*AMSA*👇

Shaik Usaimeen Rahimahullah yace:
Abunda yakamata ga Musulmi shine suyaiwata nasabarsu gwar-gwadon yanda suka Samu iko, domin hakan shine Umarni da Annabi sallallahu Alaihi Wasallam ya fuskantar dashi zuwa Al'ummarsa cikin fadinsa ( Ku Auri mata wadanda kuke qauna masu haihuwa, domin nayi alfahari dayawanku ranar alkiyama, Yawan dangi kuma shine yawan Al'ummah, yawan al'umma kuma shine izzarta da kwarjininta, kamar yanda Allah madaukakin Sarki yace: Yana gorantawa Banu Isra'ila
ﻭﺟﻌﻠﻨﺎﻛﻢ ﺃﻛﺜﺮ ﻧﻔﻴﺮﺓ، ﺍﻹﺳﺮﺍﺀ، / ٦
Muka sanyaku Masu yawa cikin mutane
Annabi Shu'Aibu Alaihissalamu yacewa mutanensa.
( ﻭﺍﺫﻛﺮﻭﺍ ﺇﺫ ﻛﻨﺘﻢ ﻗﻠﻴﻼ ﻓﻜﺜﺮﻛﻢ ‏) ﺍﻷﻋﺮﺍﻑ / ٨٦ .
Kutuna sanda baku dayawa Allah yayawaitaku
Babu wanda yake inkarin yawan al'umma shine sababin izzarta da karfinta mai-makon yanda masu mugun zato suke suranta wadanda suke daukar cewa yawan al'umma shine dalilin dake kawowa Al'umma talauci da yunwa.
Lallai Al'Ummah intai yawa tadogara ga Allah, tai Imani da Alkawarinsa zai azurtata komai yawanta kamar yanda yazo cikin fadinsa
( ﻭﻣﺎ ﻣﻦ ﺩﺁﺑﺔ ﺇﻻ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﺭﺯﻗﻬﺎ ..... ﻫﻮﺩ / ٦ .
Babu wata halitta face arzikinta yana wajan Allah
Face Allah ya saukake mata Al'amuranta ya wadatata daka falalarsa.
Dan haka bai kamata mace tai amfani da kwayoyin hana daukar ciki dasunan tsarin iyali ba saida sharudda guda biyu.
Nafarko: Yakasance tana cikin bukatar hakan dole, kamar bata da lafiya bazata iya daukar ciki kowacce shekara ba, komai siririn jikice ko kwan-kwaso, kotana da wasu ababe dazasu hanata daukar ciki kowacce shekara.
Na biyu: Mijinta yai mata izinin tasha, domin miji yanada hakkin akan 'ya'ya da daukar ciki, sannan dolene sai anshawarci likita akan wadannan kwayoyin, shin shansu yana cutarwa kobaya cutarwa.
Idan sharudda biyunnan suka cika, Babu laifi amfani dakwayoyin hana daukar ciki, Saidai hana daukar cikin nadan wani lokaci, bawai na din-din har abada ba, domin wannan akwai yanke yaduwar al'umma acikinsa.
*fatawa Mar'atul musulimah ( 2/ 657-658).*
*Illah dacutar dashan wadannan kwayoyin suke haifarwa Shaik Usaimeen yace:*
Labari ya iskeni daka bangarori dayawa daka likitoci damasu bada magani cewa kwayoyin hana daukar ciki suna cutarwa, tabangarenmu munsan illarsa, domin hana wani abu na dabi'ah da Allah yahalicci mutum akansa yakuma rubutawa matan 'yan adam babu kokwanto wannan cutarwane, Allah madaukakin sarki mai hikimane, bahaka kawai yasa jini ke fita daka jijiyoyiba awani lokaci sananne saida hikima, kasancewar Mukuma muna hana haka da wannan magun-guna cutane babu shakka.
Labari yariskeni abun yawuce yanda ake siffanta mana, yanasa lalacewar mahaifa, kuma yanasa cutukan gabobi, Wannan wajibine anisanceshi.
Tsarin iyalin da musulunci yayarda dashi shine wanda lalura tasa dole mace tadaina haihuwa, kodai saboda siranta kwan-kwasonta bata iya haihuwa dakanta, ko saboda wata cuta datasa dole tayi tsarin bisa sharudda biyun can da muka ambata.
Amma irin wanda yahudawa da 'yan bokoko suke tallatawa mutane wai ka qayyade iyalinka daka mace daya ko 'ya'a uku zuwa biyar wannan haramunne yahudancine wajibine musulmai sutashi suyaqi wannan bala'in.
Babu inda yahalatta haka kawai saboda yahudanci ma'aurata su dena haihuwa wannan ba musulunci bane.
Insuna so sudunga samun tazara daka haihuwa zuwa wata haihuwar Saisubi tsarin musulunci wajan Yaye yaro kada suke yaye yaro saiya cika shekara biyu kamar yanda alqur'ani yabasu shawara.
Sudunga yin azalu ko mula masa inzasu biya bukatar sha'awarsu dan kada ciki yashiga wannan shine tsarin iyalin da musulmai zasu iya yi amatsayin tazarar haihuwa, ba irin wanda makiya Allah yahudawa suke fesa gubarsa cikin al'ummar musulmai ba, bisa da'awar hakan nakawo talauci da yunwa, Allah yai mana tsari daka makircin kafirai yahudawa.
mijinda bayasan haihuwa saboda tsoran dawainiyar 'ya'ya kibi duk hanyar data kamata kinuna masa addinin musulunci baiyarda dahakanba, kuma ke yana cutar dake dan kinasan haihuwa, inkikai iya kokarinki yaqi kikabi duk hanyoyin daya kamata babu wani canji toki nemi yasakeki kawai babu Alkhairi atareda shi wannan amijin.
Bakiyi laifina idan kika nemi yasakeki anan, kinemi kodai yahakura kuci gaba da hayayyafa koya sakeki danke bazaki iya zama dashi ba.
Kuma aibashine zai azurtasu ba, Allah ne, kinuna masa shi sunawane agidansu ubansa shikadai ko su biyu yahaifa amma ya akai yanzu kowa yana rayuwa iya wacce Allah yaqaddara masa na arzikinsa!!
Arzikinsu ba'a hannunsa yakeba aikinsa yai tarbiyyarsu yadorasu akan hanya takwarai, shiriyarsu da arzikinsu yana hannun Allah wanda shine ya'azurta kafiri da zindiqi dajahilin dan bokon da turawa suka jirkita masa kwakwalwa.
Wallahu A'alamu.

ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ .
Post a Comment (0)