YIN AMFANI DA MAGANIN MALLAKA

*Assalamu Alaikum*
.
.


*Tambayata 7,266:*
Inada kishiyoyi biyu ya halatta nayi anfani da irin magun gunan daake anfani dasu sbd mallaka.ya zamana namiji baze iya yi maka walakanciba kuma kullum Kai yakesan gani Kaine kafi birgeshi a cikin matansa
=
=
Amsa
=
_Toh malamai dayawa sunyi maganganu akan irin wannan magani domin a larabci suna kiranshi Attiwalah. Wanda idan kuka duba cikin Kitabut Tauhid malamai suna lissafa irin wadannan magungunan cewa suna daga cikin karamar shirka wacce babu shakka haramunne. Sannan kuma irin wadannan magungunan na zamani wanda mata ayau suke gogoriyo wajan siya da siyarwa toh zeyi wuya kasamu wanda bashida illa acikin magungunan, kokarin amfanida wadannan magungunan shine yasa ayau matanmu suketa fama da wasu irin cututtuka wadanda iyayenmu duk basu sansuba. Amma idan zama da wasu matane a gidan miji ai inaga bakikai matan Annabi (s.a.w) ba wadanda kusan su tarane reras agidanshi kuma kuma kowacce tanayin bakin kokarinta wajan ganin tasamu kujerar zama a gidan Annabi, toh meyasa ke bazakiyi koyi dasuba kiyi riko da irin abunda sukayi riko dashi har suka samu wannan matsayi a wajan mijinsu se wasu magunguna haramtattu dasuke kike ganin kawai hanyarda miji ze soki?? Wannan babu shakka kuskurene kuma tunanine irinna yahudawa wadanda suke yakar zukatan matan musulmi suna rabamu da Allah ta hanyar wadannan magunguna. Amma mafi dacewa shine kiyi amfanida irin abunda matan Annabi da sahabbai sukayi amfani dashi. Amma wadannan irin magunguna shakka babu malamai sunce haramunne. Kina iya duba cikin littafin Alqaulul mufid na Usaimin kokuma ki duba cikin Fathul Majid******_
=
=
Allah Yasa mudace
 .
.
*DAGA ZAUREN*
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس تعليم الكتاب والسنة* 
📓📔 
Watsaps
08036222795
09031200070
.
°
Yau
29-08-1442
12-04-2021
=
=
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
Domin samun shafinmu a Telegram 
https://t.me/joinchat/IqYRYUcyJstfI3sSYKPKsQ
°
Kuna iya samun tsoffin darussanmu kai tsaye ta cikin wannan shafin
http://zaurenkitabuwassunnah0.blogspot.com
*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ اللهم ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ*
.
*Subhanakallahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illa anta astagfirukallahumma wa atubu ilaika*
Post a Comment (0)