WACE CE RUMAISA? 4 & 5


WACE CE RUMAISA (UMMU SULEIM)
  
                             ❓

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

FUTOWA TA 👇
      (4), (5)


YAYANTA DA LABARIN MUTUWAR DANTA

   Ummu suleim ta haifi yara guda uku duk maza biyu na abu dalha daya kuma na malik shi ne anas wanda ya kasance yana yiwa manzan Allah (saw) hidima har zuwa lokacin da manzan Allah (saw) ya bar duniya, wadannan sune "yayanta. 

  labarin mutuwar danta ya kasance kamar yadda yazo acikin bukhari da musulim, wata rana dan gidan abu dalha bashi da lafiya kuma abu dalha ya kasance yana sansa so mai tsanani, abu dalha ya kasance kullum idan gari ya waye yana alwala yaje masallaci, bayan ya yi sallar asuba zai zauna tare da manzan Allah saw har zuwa kusan rabin rana sai ya dawo gida ya yi baccin qailula sai yaci abinci, idan kuma ya yi sallar azahar sai ya shirya ya futa bazai dawo ba sai bayan sallar isha'i. 

Wata rana abu dalha ya futa zuwa masallaci bayan sallar azahar sai wannan yaran ya mutu, sai 🌹ummu suleim🌹tace da mutanan gidan kada wanda ya bawa abu dalha labarin mutuwar dansa nice zan gaya masa, abu dalha ya dawo gida tare da wasu daga cikin mutanen da suke tare a masallaci sai yace mata ya ya dana sai tace ai ya kasance cikin nutsuwa sama da yadda ya kasance abaya kuma ina fatan ya huta sai ya yi tunanin yaran ya samu lafiya, sai ta kawo musu abincin dare sukaci bayan sun watse, abu dalha ya shigo gida sai tayi masa ado da kwalliya tayi masa abubuwan da zata ja hankalinsa sama da yadda take masa har tayi rinjaye agaresa ya kusance ta, ya yin da qarshen dare ya yi sai tace masa ya kai aba dalha yanzu ace wasu mutane subaka ajiyar kaya sannan suzo su tambayeka kayansu zaka hanasu? sai yace mata a'a sai tace to ubangiji ya baka aro na danka kuma yanzu ya karbi yaran ka nemi lada wajansa sannan kayi haquri, sai fushi ya ka masa sai yace yanzu kika gyaleni har abun da ya faru ya faru sannan ki bani labarin mutuwar dana sai ya yi istirja'i ya yi godiya, ya yin da asuba tayi sai ya yi wanka ya tafi masallaci ya yi salla tare da manzan Allah saw sai ya basa labarin duk abun da ya faru sai yace kun raya wannan daran naku,sai yace eh, sai yace ubangiji ya sanya muku albarka cikin wannan daren naku, sai ta dauki ciki. 

Wata rana manzan Allah saw ya kasance cikin wata tafiya alokacin tana tare dashi ya yin da suka dawo daga wannan tafiyar sun kusa zuwa madina sai na quda ta kamata, sai abu dalha ya tsaya wajanta manzan Allah saw ya tafi, sai abu dalha yace ya ubangiji kasani ina matuqar san idan zan futa wata tafiya na futa tare da manzanka haka zalika idan zan dawo na dawo tare dashi yana nufin (YAQI) yanzu kuma kana ganin abun da ya tsareni, kwatsam sai 🌹ummu suleim🌹 tace ya aba dalha yanzu fa na daina jin abun da nake ji, sai suka tashi suka tafi suna zuwa madina sai na quda ta dawo sai ta haifi yaro na miji, sai tace ya kai Anas dauki wannan yaron ka tafi dashi wajan manzan Allah saw kada wanda ya bashi wani abu har sai kaje dashi wajansa ta tura tare dashi dabino, ya yin da safiya tayi nayi sauri na tafi dashi wajan manzan Allah saw yana ganinsa sai yace dani "yar gidan milhan ce ta haihu sai nace eh, sai yace miqosa sai yace akwai wani abu a tare da kai sai nace eh dabino sai ya karba ya tattauna abakinsa sai ya yi masa tahniki ya sanya acikin bakin yaron, farkon abun da ya fara shiga cikin yaron yawum manzan Allah saw tare da dabinon da ya tauna, sai nace ya manzan Allah saw a saka masa suna sai ya shafi fuskar yaron ya saka masa suna Abdullahi, babu wani yaro agarin madina da ya kaisa falala, kuma ta tsatsan wannan yaron an samu kusan mutane guda goma duk hafizan Alqur'ani kuma aqarshe shima wannan yaron ya yi shahada a kasar faris.


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

MU HADU A FUTOWA TA 06

Rubutawa... ✍️✍️✍️✍️✍️
         Dalibi mai neman ilimi Nazifi Yakubu Abubakar
             (Abu Rumaisa)
          🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)