ANNABI DA SAHABBANSA // 77



ANNABI DA SAHABBANSA // 77
.
Mawallafi: Baban Manar Alqasim
.
MUSULMAI AN SHIGA WANI HALI
Rundunar da ta fito wa musulmai ta bayan gida ta yi mummunar ruguza musu lissafi, don suna fada da wata ne a gaba, ga wata ta fito ta baya, masamman kasancewar ta bayan duk da qanqacinta ta fi ta gaban masifa, sai ya zamanto yanzu qwatar kai kawai za a yi, ko dai takobinka ya qwace ka, ko qafarka ta taimaka maka, da wannan sai lissafin ya rikice gaba daya ya zamanto an shiga halin-ni-'yasu.
.
Rundunar muslunci ta shiga matsala don:-
1) Yawansu ba daidai yake ba ko kadan, 3,000 ne da 700.
2) Dama mushrikai su ke bangaren Madina, musulman ne a bangaren Makka, in ya kasance qarfi yana hannun mushrikai to sai yadda hali ya yi, halin da ake ciki kenan yanzu, ba da jimawa ba aka fita daga hannun mushrikan nan, ko ba su kashe mutum ba in ya shiga hannunsu Allah kadai ya san yadda za su yi da shi, to bare an kashe su a Badar ba kadan ba, qila mutum ya gudu ya sami inda zai bauta wa Allansa shi kadai.
.
3) Wasu daga cikin rundunar sun yi wannan tunanin don haka suka ja da baya suka hau dutse, wasu kuma suka koma Madina sabo da wani cece-kuce.
4) Wasu cikin rashin sani sun fada cikin mushrikai suka fara yaqi da junansu ma ba tare da sun ankara ba, tabbas an shiga wani hali, ko ba komai an dauki darasi don an san mafarin lamarin.
.
Gaskiya na qarshen nan sun fi shiga halin ha-u-la'i don ma ba su san inda za su dosa ba, in ma guduwa aka ce sun yi dole ya janyo hakan masamman in aka lura da halin da aka sami kai a ciki, abin ma da ya qara wa Borno dawaki kwatsam sai suka ji cewa an kashe Manzon Allah SAW, nan take dan sauran abin da ke hannunsu ya salwance, in ma yaqin mutum ya ce zai yi sai ya yi wa kansa bayanin dalili.
.
Wasu dai sun fasa yaqin sun dauki hanya, gaskiya ba guduwa suka yi don tsoro ba kamar yadda maqiya muslunci suke yayatawa, wasu kuma suka watsar da makaman gaba daya, wasu suka yi tunanin tuntubar Abdullah bn Ubay don ya dakatar da Abu-Sufyan su sun miqa wuya, an kashe Annabi SAW, yaqi ya qare, sai ga Anas bn Nadeer ya ce "Me kuke jira ne?" Suka ce "An kashe Manzon Allah SAW"
.
Nan ya ce "To meye amfanin rayuwa bayan mutuwarsa? Ku miqe kawai ku mutu a hanyar da shi ma ya mutu" sai ya juya yana cewa "Allah ina miqa hanzarina a kan abin da musulmai suka yi, ina tsame kaina daga abin da kafurai suka yi" sai ya qara gaba, Sa'ad bn Mu'az ya hango shi ya ce "Sai ina Abu-Umar?" Ya ce "Ga qamshin aljanna can yana busowa ta Uhud" haka ya yi ta fafatawa har aka kashe shi, ba wanda ya gane gawarsa sabo da tsabar sara da suka, sai 'yar uwarsa ta gane shi ta dan yatsarsa.
.
Sai Thaabit bn Dahdaah ya daga murya yake cewa "Ansarawa Muhammad dai tabbas an kashe shi, amma Allah kam a raye yake kuma ba zai mutu ba, ku yi yaqi sabo da addininku, lallai Allah zai ba ku nasara kuma ya taimake ku, nan take ya zaburar da wasu suka fuskanci rundunar Khalid, har dai aka kashe su gaba daya, sai wani Muhajiri ya sami wani Ba'ansare faca-faca cikin jini yake tambayarsa.
.
Ya ce "A ganinka an kashe Muhammad?" Ba'ansaren ya ce "Ko ma an kashe shi ya dai isar da saqo, ku yi yaqi kawai ku kare addininku" (Asseera Alhalabiyya 2/22) a hankali musulmai suka fara samun kansu, qarfinsu ya fara dawowa, suka fara farfadowa, yadda za a fahimci cewa dama jarabawa ce kawai daga Allah SW, duk da cewa nasara na tare da su amma sai sun tsaya.
.
Nan take kowa ya dauki makami, aka kawar da zancen samun Ibn Ubay, aka sake fuskantar abokan gaba, don duk da wannan tsaka mai wuyar Allah SW bai ba su damar tsaga tsakiyar musulmai ba, aka gano cewa Annabi SAW dai yana da rai bai mutu ba, qarfi ya qaru, suka fita daga tsakiya suka dawo da kafurai gefe guda, sai qoqarin qwato Annabi SAW suka yi, a gaba akwai: Abubakar, Umar, Aliy da sauran manyan sahabbai.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)