HUKUNCIN KORAR YARO DAGA MASALLACI
:
*TAMBAYA*❓
:
Menene hukuncin korar YARO daga masallaci, ko daga sahun farko don BABBA ya maye gurbinsa?
:
*AMSA*👇
:
Idan yaro ba ya cutar da kowa – da aikinsa ko maganarsa to bai halarta a fitar da shi daga masallaci, ko a dawo da shi sahun da yake baya da wanda yake tsaye a cikinsa ba, koda kuwa a bayan liman yake kai tsaye; saboda a sunna wanda ya fara zuwa wuri shi ya fi cancanta da shi, kuma Annabi (SAW) ya hana mutum ya tashi danuwansa daga wurinsa shi don ya zauna a wurin, masallatai kuma gidajen Allah ne, bayin Allah (baba da yaro) daya suke a cikinsu. Hadisin da Annabi (SAW) yake cewa “Masu hankalin cikinku ya zama su suke biye da ni a sahu” kuwa ba ya nuna a rika korar yara daga sahun farko koda daga su sai liman kamar yadda wasu malamai suka dauka. Wannan hadisi yana kwadaitar da manyan ne kan su je masallaci da wuri don su samu tsayawa a bayan liman. Sannan korar su daga sahun da suke zuwa na baya zai haifar da matsaloli kamar: Taruwarsu a wuri guda wanda wannan zai sa su yi ta wasa da hayaniya lokacin sallah Za su rika kin Masallaci Za su rika kin masallata, musamman mai korar su.
Shiekh Ibn Uthaimin
Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaɗa wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, _Amma don girman ALLAH kada ku kwafa ku goge wani abu daga ciki. Kuji tsoron ALLAH
Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
