Ƴar Bautar Ƙasa 26


*👩🏻‍💼Y'AR BAUTAR K'ASA*


Zahra Muhammad Mahmud


DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION


*Yasmin tafeesu natayaki murnar kammala littafinki na bakar alada,Allah yasa kifi haka,Allah kuma yakara haɗa kanmu up up up da bazarmu writers association,atare abuge ba dama,abari mu wuce ga haushi,taken mu kenan*

*26*


Suna tafe bawanda keyiwa wani magana salma se danne danne take awaya hankalinta kwance,waigowa najeeb yayi ya kalleta yayi tsaki sannan yace.

"jibeta don Allah,sekace ba ita bace take ta rusa kuka ɗazu,ashe na munafunci ne"

Ɗago idonta tayi tayi masa fari cikin wani salo,wanda ya haddasa kan motar kusan kwacewa a hannun najeeb dan har sun sauka a titi.

Da sauri yadawo kan titi,su kabeer dake binsu abaya har sun fara sallallami.

Murmushi salma tayi sannan tace.tana ƙara kaɗa masa ido.

"to dan kuma nayi kuka ɗazu cemaka akayi dauwama zanyi inayin kukan,wancenma danayi dan kar ace banyi bane"

Tsaki yasake yi yace.


"Allah de ya tsinewa munafuki,kuma naga alamun kina cikinsu"

Shewa salma tayi sannan tace.

"doctor kenan,ay gwanda kalar nawa munafunci,so dubu akan naka,sabida ni nawa be illatani ba"

Wani uban birki yaja,sannan ya koma gefen titi yayi parking.

Jawota yayi jikinshi da ƙarfi ya zazzare mata ido gami da cukuikuyeta acikin gyalen data rufa,yace.

"Ni ne munafukin?munafuncin me nayi da har ya illatani?"ya faɗi cikin fushi.

Ido salma tashiga zarewa,dan gani take dukanta zeyi.

Su kabeer parking sukayi suma fitowa yayi ya nufo motar dan ganin meke faruwa,ta glass din gaban motar yaleƙa ganin salma rungume jikin najeeb ne yabashi dariya wato soyewarsu sukeyi shiyasa suke tsayawa,

Juyawa yayi kawai yakoma motarshi yaja yayi gaba abunshi,koda yan uwan salma suka tambayeshi murmushi kawai yayi yace.

"kunsan yau yafito dags asibiti so yagajine shine yake ɗan hutawa"

Shuru sukayi shi kuma yaci gaba da tuƙinshi.

shiko najeeb yaƙi sakinta wai dole se ta faɗa masa munafuncin da yayi har ya illata shi.

Kuka salma tasa masa na shagwaɓa tana ƙoƙarin kwacewa daga ruƙon daya mata shi kuma yaƙi sakinta.

Nanfa suka shiga kokawa,har cikin saa hannun najeeb ya sauka akan boobs ɗin salma.

taushinsune yasa najeeb sakinta da hanzari yaja gefe yana bin boobs din da kallo,yana tunanin inda yaji taushin,

Salma komawa gurin zamanta tayi tana zumɓuro baki.

Najeeb kamar wanda shocking yaja sam yakasa motsin kirki kawai ya kafe ƙirjinta da kallo,bin idonshi salma tayi ta gane inda yake kallo ajikinta,dan haka da sauri ta kife fuskarta akan cinyarta.

Se lokacin najeeb yadawo daga inda yatafi,jiki asanyaye yatada motar suka ci gaba da tafiya.

Har suka isa kano bawanda yasake magana.

Suna isa jamaa suka zagaye motar anayiwa amarya sannu da zuwa.

kai tsaye gurin hajiya kaltum aka kaita aka damƙa amanarta,sannan aka je gurin mahaifin najeeb da ita yamusu addua sosai,daganan aka kaita parta dinta,

Ɗan ƙara gaggara gidan yan uwan nata sukayi sannan kabeer ya kwashe su zuwa kaduna dan ba kwana zasuyiba.

Haka suka tafi suka barta tana ta rusar kuka.

Najeeb be shiga gidan ba se bayan sallar ishai,koda yashiga a falo yasami salma tana kuka,tsayawa yayi yana mata kallon mamaki,kasa jurewa yayi yace mata.

"kince wancan kukan kinyine dan kar ace bakiba,shi kuma wannan da kikeyi tun ɗazu na uban menene?"

ɗago ido tayi ta wurga masa harara,gamida murguɗa masa baki tace.cikin kukan,


"shima wannan irin wancanne,meye damuwarka?"

"Damuwata kidena kukan dan kin cikamin kunne,"

"in bandena ba me zaka iya yi?"

"wlh na jaki zakici,danni banason hayaniya"

Ayko salma ɗaga sauti tayi na kukan harda shure shure da ƙafa.

Najeeb gurinta ya nufa cikin fushi,ganin hakane yasa salma kwasawa da gudu,ta haura sama inda ɗakinta yake,mara mata baya najeeb yayi shima da gudun,dan so yake ya koya mata hankali.


muje zuwa.

Surbajo for life.

Post a Comment (0)