KOKONTON FITAR ISKA (TUSA) A CIKIN SALLAH.

KOKONTON FITAR ISKA (TUSA) A CIKIN SALLAH.



Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allαн(ﷻ), muna gode masa, muna neman taimakonSa da gafararSa, kuma muna neman tsarinSa daga sharrukan kawunanmu da munanan ayyukanmu. Haqiqa duk wanda Allαн(ﷻ) Ya shiryar babu mai iya 6atar da shi, wanda kuma Ya 6atar babu mai iya shiryar da shi. 

Ina shaidawa babu abin bautawa da cancanta da gaskiya sai Allαн(ﷻ), kuma Annabi Muhammad (ﷺ) bawanSa ne, kuma manzonSa ne. 

'Yan uwana musulmi! Tabbas abu ne sananne cewa, mutane dayawa suna fama da shakku da kokonto a lokacin da suke sallah, musamman a wannan lokaci da muke shagala da wasu ayyukan a cikin sallolinmu, mutum ne zai ji kamar iska ta fita ta duburarsa, amma be tabbatar da fitan nata ba, don haka ne na ga ya dace in yi rubutu a kai don qara wa juna ilimi dangane da wannan shubuha. 

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ، قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم ‏ ”إِذَا وَجَدَ أَحَدُكُمْ فِي بَطْنِهِ شَيْئًا فَأَشْكَلَ عَلَيْهِ أَخَرَجَ مِنْهُ شَىْءٌ أَمْ لاَ فَلاَ يَخْرُجَنَّ مِنَ الْمَسْجِدِ حَتَّى يَسْمَعَ صَوْتًا أَوْ يَجِدَ رِيحًا“.‏ أخرجه مسلم. 

An kar6o daga Abu Huraira (R.A) ya ce: Mαnzon Allαн(ﷺ) ya ce: “Idan ďayanku ya ji wani abu a cikinsa, sai ya yi kokonto a kansa; shin wani abu ya fita daga cikinsa kokuwa? To kada ya fita daga masallāci har sai ya ji sauti ko ya ji wani wari.” Muslim ya ruwaito shi. 
.

روى البخاري (137) مسلم (361) أنه شُكِيَ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الرَّجُلُ يُخَيَّلُ إِلَيْهِ أَنَّهُ يَجِدُ الشَّيْءَ فِي الصَّلَاةِ. قَالَ : (لَا يَنْصَرِفُ حَتَّى يَسْمَعَ صَوْتًا أَوْ يَجِدَ رِيحًا).

Bukhari ya ruwaito a hadisi mai lamba 137, da Muslim 361 cewa, wani mutum ya kai kukansa wajen Mαnzon Allαн(ﷺ), yana kokonton lallai shi ya ji (alamun fitar) wani abu a cikin sallah. Sai (Annabi) ya ce: “Kada ka yanke (sallar) har sai ka ji sauti ko wari.”

Wato idan masallāci ya ji alamar fitar iska daga duburarsa, to hakan ba zai sa ya yanke sallarsa ba har sai ya samu yaqini a kan fitar tusa, domin wannan yana daga cikin shakku da shaiďan yake cusawa a zukatan masallāta don ya lalata masu ibadarsu. 

عَنِ اْبْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اَللَّهُ عَنْهُمَا; أَنَّ رَسُولَ اَللَّهِ صلى الله عليه وسلم قَالَ: ”يَأْتِي أَحَدَكُمُ الشَّيْطَانُ فِي صَلَاتِهِ, فَيَنْفُخُ فِي مَقْعَدَتِهِ فَيُخَيَّلُ إِلَيْهِ أَنَّهُ أَحْدَثَ, وَلَمْ يُحْدِثْ, فَإِذَا وَجَدَ ذَلِكَ فَلَا يَنْصَرِفُ حَتَّى يَسْمَعَ صَوْتًا أَوْ يَجِدَ رِيحًا“. أَخْرَجَهُ اَلْبَزَّار.

An kar6o daga Ibn Abbas (R.A), lallai Mαnzon Allαн(ﷺ) ya ce: “Shaiďan yana zuwa wa ďayanku a cikin sallarsa, sai ya busa iska a cikin duburarsa, sai ya sa masa kokonton ya yi tusa, kuma bai yi tusa ba, idan (ďayanku) ya ji haka, to kada ya katse (sallarsa) har sai ya ji sauti ko wani wari.” Bazzār ya ruwaito shi.

Shaiďan yana 'koƙarin shagaltar da mai sallah daga sallarsa da kokonto da shakkun da zai rinjaye shi a sallarsa, daga cikin waďannan wasi-wasin akwai wanda ya shafi tsarkinsa, har sai ya bar mai sallah a cikin wasi-wasi game da tsarkinsa, shin na yi tusa ko ban yi ba? sai ya yanke sallarsa ba tare da ya tsinci komai a cikinta ba. Kun ga ya jawo masa asara. Da irin wannan wasi-wasi ne shaiďan ke cire wa mutum soyuwar sallah a cikin zuciyarsa, sai ya kasance mutum sai ya wahala sosai kafin ya yi sallar da zai gamsu da ita. 

Duk wanda ya yi tusa yayin da yake sallah, kuma yana da yaqini a kan cewa tusa ya yi, ta hanyar jin sautin fitarta ko warinta, to zai yanke sallah ya je ya yi alwala ya sake sallarsa, amma wanda ba shi da yaqini ko tabbacin cewa tusa ce ta fita, kuma a lokacin da ya ji alamun fitar wani abu daga duburarsa bai ji wani sauti ko wari ba, to zai ci gaba da sallarsa ne ba zai yanke ba. 

Hakim ya ruwaito daga Abu Sa'id (marfu'an) cewa:

”إذا جاء أحدكم الشيطان، فقال: إنك أحدثت. فليقل: كذبت“.

“Idan shaiďan ya zo wa ďayanku ya ce: lallai kai ka yi tusa. To ya ce: 'Karya kake”.

Kuma Ibn Hibban ya fitar da shi da lafazin:

”فليقل في نفسه“.

“To ya faďa a cikin zuciyarsa”.

Wannan hadisi na 'karshe yana nufin:

((Idan shaiďan ya zo maku)): wato idan ya zo maku a cikin sallah. ((Sai ya ce lallai ka yi tusa)): abin nufi, sai ya sa masa wasi-wasin cewa ya yi tusa. ((To ya ce: 'Karya kake)): ma'ana ya faďi a cikin zuciyarsa, kamar yadda ya zo a ruwayar Ibn Hibban. 

Idan muka duba waďannan hadisai, za mu ga dai cewa duk fashin baqine suke yi qarqashin hadisin Abu Huraira. Kada mutum ya sake ya bar sallah don yana wasi-wasi a kan fitar tusa har sai ya samu yaqini a kan fitarta. 

'Yan uwa mu sani! Wajibine mu yi iya bakin 'kokarinmu don guje wa wasi-wasin shaiďan, domin burinsa be wuce ya lalata mana ibadarmu ko ya rage mana ingancinta, ko kuma ya sa ayyukan ibadah su dinga mana wahala. 

Daga cikin hanyoyin da za mu bi don ku6uta daga wasi-wasin shaiďan, akwai neman tsarin Allαн(ﷻ) daga sharrukansa ta hanyar addu'o'i da karanta suratun Nas, saboda fadin Allah:

”مِن شَرِّ الوَسوَاسِ الخَنَّاسِ“

“Daga tsarin mai sanya wasi-wasi...” Al-Qur'an 114: 04.

Sannan mu dinga kyautata alwalarmu, mu kasance muna tattara tunaninmu waje ďaya izuwa ga Allah a yayin da muka tsayu a sallah, sannan mu je gaban malamai mu nemi ilimi game da sharuddan sallah da yadda Mαnzon Allαн(ﷺ) ya kasance yana sallarsa. 

Ina rokon Allah Ubangijin mutane, Mamallakin dukkan komai da Ya kare mu daga sharrukan mutum da aljan da sharrukan kawunanmu, kuma Allah Ya tabbatar da mu a kan dai-dai. Fatanmu shi ne mu gudu tare mu tsira tare. 

والله هو العليم الحكيم.

*✍🏾Ayyub Musa Giwa.*
*ANSAR.*
*17th Aug, 2020.*
🕌Irshadul Ummah WhatsApp.
*+2348166650256.*

Wassalamu alaikum Warahmatullah.

1 Comments

  1. Through cloud gaming, players can gain access to virtual machines stored by the on line casino in the cloud. Blackjack is 코인카지노 mostly thought-about the type of gambling with the best odds. Ignition’s poker expertise works nice on cell and PC, so that you never have to worry about it being too far out of reach.

    ReplyDelete
Post a Comment