MIJINA YANA SADUWA DANI TA DUBURA

MIJINA YANA SADUWA DANI TA DUBURA


*TAMBAYA*❓
:
Dan Allah ina bukatar ku ɓoyeI'D ɗina saboda kare mutunci na da na mijina.
Yau shekarar mu ɗaya da 'ƴan watanni kenan da yin Aure mu.., Akoda yaushe Mijina yafi son yin Jima'i dani ta baya. wai acewar sa yafi jin daɗi
kuma buƙatar shi tafi biya.,
Naje wajen wata walimar ƙawata naji wani Malami da aka gaiyaceshi yin wa'azi yace ba
Kyau yi ta baya.. Koda nasanar wa Mijina yace wai in Rabu
dasu Ƙarya sukeyi ai ance Matarka gonarka ce ka shigeta duk ta inda kake so.
TO DON ALLAH YAYA LAMARIN YAKE???
:
*AMSA*👇
:
Yadda lamarin yake, Idan Saduwar da kukeyi ta dubura ne, to Wannan HARAMUN NE.
Saboda Allah ya sanya mana dalilin Saduwar Jima'i abisa manufofi ne guda biyu.

1. Na Farko domin samar da zuriyyah Halastacciyya. shi yasa ma Allah (swt) yace MATAYENKU GONAKINKU NE.
Abinda Ake nufi anan Farjinsu shine Gonar da ake yin shukar aciki. Maniyyin mazaje shine IRIN DA AKE SHUKAWA.
'YA'YAN Da aka haifa sune AMFANIN GONAR.

Don haka be halatta ayi Jima'i ta dubura ba saboda Dubura BA WAJEN DA AKE DAUKAR CIKI
BANE.. Kuma duburar Dan Adam anyita ne domin fitar da Ba-haya, ba domin Jima'i ba.
Allah yana cewa : "KUZO MUSU TA INDA ALLAH YA UMURCE KU" Shi kuwa Allah ya umurce mazaje nesu sadu da matayensu ta farjinsu ba ta dubura ba.

2. Dalili na biyu na saduwar Jima'i shine domin Abiya wa juna bukatarsu ta jinsi da
jinsi. Ita kuwa saduwa ta dubura ba zata gamsar
da matar ba. ko da shi mijin yana jin cewar ya gamsu.
Wasu malaman ma sunce dalili ɗaya ne yake sa asadu da mace: don haifar da zurriyya ba
wai don biyan bukata ba kadai.
Abinda yake Halastacce shine: Miji zai iya saduwa da matarsa ta baya, AMMA TA CIKIN FARJINTA BA TA DUBURA BA.. Wannan halal ne.

Annabi ﷺ yace: "DUK WANDA YA SADU DA MATARSA TA DUBURA TSINANNE NE".
(Abu dawud da Nisa'iy ne suka ruwaito shi.
kuma Sahihi ne Ligairihi).
An ruwaito wannan hadisin ta hannun Sahabbai masu yawa sosai. acikinsu akwai:
Sayyiduna Aliyyu bn Abi Talib (ra).
* Abu Hurairah
* Umar bn Alkhattab.
* Talqu bn 'Aliyyin
* Khuzaymah * Aliyyu bn Talqin.
* Ibnu Mas'ud.
* Ibnu Abbas.
* 'Uqbatu bn Aamir.
* Jabir bn Abdillah.
* Albarra'u bn Aazib. * Abdullahi bn 'Amr
* Anas bn Malik.
* Abu Dharrin Al_Giffary (Allah ya yarda dasu).
Duk da cewa akwai kalamai akan hanyoyin hadisan, Amma kuma hanyoyin suna Qarfafar
Junansu. Wannan Ayar wacce mijin naki ya dogara da ita, (Ku zowa gonakinku ta yadda ku ka so).
Ki gaya masa be fahimci ayar bane. kuma be san dalilin saukarta bane. domin kuwa ayar tana nufin cewar -
"Ku sadu da matayenku Akwance, ko atsaye, ko a tsugunne, ko azaune, kota gaba ko ta baya, AMMA TA FARJINSU.. BA TA DUBURA BA.
Shi yasa ma ɗaya ayar take cewa: "KU ZO MUSU TA WAJEN DA ALLAH YA UMURCE KU".
Ayar ta sauka ne yayin da wasu Sahabbai suka tambayi Manzon Allah ﷺ akan wata maganar da sukaji awajen Yahudawa. wai
Idan mutum ya sadu da matarsa ta baya Amma ta farjinta, Idan ta samu ciki ahaka, wai Za'a haifi yaron da Juyayyen idanu (Harara-Garke).
Don haka Allah ya saukar da Ayar domin ya Qaryata maganar Yahudawa.
Ki gaya masa Cewar Dukkanin Maluman Maz_habobin nan huɗu da ma wasunsu Sunyi
ittifaqi akan haramcin saduwa ta dubura gaba ɗaya.
Ki gaya wa Mijinki cewar Idan be dena ba, WALLAHI MANZON ALLAH ﷺ YACE: "DUK WANDA YAYI JIMA'I DA NAMIJI, KO KUMA YA SADU DA MACE TA DUBURARTA, ALLAH BA
ZAI DUBESHI DA RAHAMA BA".

YA ALLAH KA TSAREMU KA KIYAYEMU. AAAAMEEEEEN.

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING wasu da yawa zasu amfana.

2 Comments

Post a Comment